TARIHIN MARIGAYI SHEIKH Dr. ALI MUSTAPHA MAIDUGURI.
An haifi Sheikh Dr. Ali Mustapha a anguwar Fezzan dake
Maiduguri a shekarar 1968. Mahaifin shi (Alhaji Shettima Bukar
Mustapha Konduga) dan asalin Kwanduga L. G. A ne,
mahaifiyar shi (Hajiya Yakaka Bukar) 'yar asalin garin Dikwa
LGA ce.
.
Shi dai Dr. Ya fara karatun shi na farko a wurin mahaifin shi
inda yafara da karatun Tahiya, Sallah da Al-qunutu. Daga
bisami yashiga makarantar Allo (tsangaya) a wajen wani
malami mai suna 'Mallam Awa' a nan Fezzan a shekarar 1972,
yayi karatu har zuwa lokacin da malamin nashi ya samu larurar
tabin kwakwalwa sakamakon hatsarin mota. Hakan yasa
mahaifin shi yasa shi a makarantar Islamiya mai suna
'Madarasatul Nurul Atfan' wadda a yanzu aka canja mata suna
'Usman Islamiya School' a shekarar 1975.
Bayan ya kammala Aji biyar (class 5) a wancan lokacin, sai
Mallam ya garzaya zuwa High Islamic Collage Maiduguri a
shekarar 1982, inda yayi shekaru hudu (4) a matakin secondary,
daganan yaci gaba da karatun Diploma a Fannin Hausa,
Larabci da Shari'a a wannan makarantar. Bayan ya gama a
shekarar 1990, sai aka musu jarabawar daukan malamai inda
yasamu nasarar zama malami a nan 'High Islamic college a
mataki na grade ll teacher.
Malam ya kwashe shekaru bakwai (7) yana karantarwa,
daganan yasamu cigaba zuwa Jami'ar Musulunci ta Madina a
shekarar 1997, sakamakon jinya da yayi wadda tayi sanadiyyar
jinkirin zuwa, hakan yasa hukumar Makarantar ta ajiyeshi a
Matakin 'Shu'ubah' (remedial) inda yayi shekara daya daganan
yasoma karatun shi a fannin 'Shari'a law' da harshen larabci
anan ma malam yayi shekaru hudu (4). Kammalawar shi keda
wuya, sai malam yanemi damar cigaba da karatun shi na
'Masters degree' a Fannin Uslul Fiqihi. A jarabawar da suka
rubuta, malam ne yazo na daya a cikin daliban da suka zo daga
Nigeria a shekarar 2002, amma bai samu damar fara karatu a
wannan shekarar ba sabo da mutum biyu (2) kacal aka dauka a
cikin mutane 27 da sukaci jarabawar daga kasashe daban -
daban.
Daganan malam yadawo gida Nigeria inda yafara karatun
National Diploma a makarantar El kanemi Collage dake
Maiduguri a fannain 'Shari'a' a shekarar 2003. A shekarar 2004
kuma, malam ya garzaya Jami'ar JOS inda yayi karatun shi na
Masters a fannin larabci, kuma yayi nasarar kammalawa a
shekarar 2006. A shekarar 2015, malam ya fara PhD a fannin
larabci a Jami'ar Jahar Nasarawa (Nasarawa State University)
inda ya kammala a shekarar 2017.
SASHIN AIYUKA.
* Malam ya taba zama grade ll teacher a shekarar 1990 - 1997
* Limancin Sallolin Juma'a da na Idi na tsawon shekaru 25
* Malam yayi aiki a matsayin Director Shari'a, a ministry of
religions affairs Borno State. 2005 har zuwa rasuwarsa
* A mataki na kungiya kuma, Malam shine shugaban Majalisar
Malamai na farko a mataki na MMC, sannan shugaban majalisar
malamai na jahar Borno. Saboda himmar sa kan lamarin addini,
Sheikh Ali Mustafa an zabe shi member na majalisar koli ta
kasa shekaru da dama kafin Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau ya
nadashi matsayin babban Sakataren Majalisar Malamai na
kungiyar ta kasa bayan rasuwar Sheikh Dr. Al Hassan Sa'id
Jos.
Sheikh Ali Mustafa mutum ne da aka sanshi da cika alkawari,
kyautatawa, da rikon amana.
Muna fata Allah ya jikan sa da rahama kuma jannatul fir-dausi
ya zama Shine makomarsa ameen.
Sheikh Ali Mustafa ya bar mata daya da 'ya'ya 15 a Duniya.
Friday, May 24, 2019
Home
Unlabelled
TARIHIN MARIGAYI SHEIK DR. ALI MUSTAPHA MAIDUGURI.
TARIHIN MARIGAYI SHEIK DR. ALI MUSTAPHA MAIDUGURI.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
ads1
Author Details
new platform in northern arewa
No comments:
Post a Comment