Shugaban kasa Buhari zai shilla zuwa birnin Makkah da
Madinah ranar Al-hamis mai zuwa domin halartar taron
'Kungiyar 'kasashen Musulmi ta duniya" watau OIC ko kuma
"Organization of Islamic Countries".
Taron da aka saba yi duk shekara a kasashe daban daban, na
bana za'a tattauna akan abubuwan da suke addabar kasashen
Musulmi da kuma nemo hanyar magance kuncin rayuwa a
kasashen Musulmi dake fadin duniya.
Wannan taro na zallan Musulmi da kuma 'kasashen Musulmi
domin, sannan shugabannin zasu duba batun me yasa fitinar
kashe kashe dake yayi yawa a kasashen Musulmi?
sai dai tun a shekara ta 2016 da shugaba Buhari ya Sanya
Nigeria a cikin 'Kungiyar 'kasashen Musulmi ta Duniya ake
sukan sa da kuma zargin yana son mayar da Nigeria kasa mai
bin tsarin Musulunci, sai dai fadar shugaban kasar tace sam ba
haka bane.
Ko kwanaki 6 da suka wuce tsohon shugaban kasa Olusegun
Obasanjo yayi hira da 'yan jaridu cewa "Tabbas ana yunkurin
dora Nigeria akan dokokin Musulunci, wanda mu kuma baza mu
yarda da wannan makircin ba, shekaru 4 kenan ba'a tsinana
komai a kasar ba, sai kokarin kawo tsarin wani addini".
Masu sukan Buhari akan lamarin suna cewa ai Nigeria babu
ruwan ta da bin wani addini kamar yadda sashen na 10 na
Constitution ya bayyana, dan haka suke cewan bai kamata ya
fifita addinin sa a zahiri akan wani addini ba, abin mamaki 'yan
uwan sa Musulmi sune akan gaba wurin sukan sa akan haka,
suna cewa halartar taron kungiyar 'Kasashen Musulmi da
Buharin zai yi aikin banza ne.
Friday, May 24, 2019
Home
Unlabelled
SHUGABAN ƘASA MUHAMMADU BUHARI, ZAI SHILLA ZUWA BIRNIN MAKKA DA MADINA RANAR ALHAMIS MAI ZUWA.
SHUGABAN ƘASA MUHAMMADU BUHARI, ZAI SHILLA ZUWA BIRNIN MAKKA DA MADINA RANAR ALHAMIS MAI ZUWA.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
ads1
Author Details
new platform in northern arewa
No comments:
Post a Comment