Wani bawan Allah ya bayyana a shafin sada zumunta na facebook cewa, abin da ya gani a dai-dai tashar Kawo na garin Kaduna ranar Litinin 20-5-2019, ya ba shi tsoro matuƙa. Bawan Allah ya ce, Masu garkuwa da mutane ne suka je gidan wani bawan Allah suka kama shi tare da yaronsa, suka saka su a mota sannan suka tafi da su. To amma a lokacin da wannan al'amari ya faru, wani ɗan Achaɓa yana kallonsu, sai ya rugo a guje ya sanar da mutane a tashar Kawo halin da ake ciki.
Ko da jin wannan labari, sai nan da nan mutane suka toshe hanƴar. Kwatsam sai ga masu garkuwa da mutanen sun biyo wajen da motar, amma sai suka ga jama'a damƙam babu hanƴar wucewa. Yayin da masu garkuwa da mutanen suka fahimci cewa wa su aka toshe hanƴar, sai suka fara harbi da bindiga domin a watse su samu su tsere. Nan take sai ga Sojoji da Ƴan sanda sun bayyana a wajen, yanke-take jam'in suka harbe mutum biyu daga cikin masu garkuwa da mutanen, dama su uku ne. Sai ɗayan ya tsere ya shiga gidan man Oado, mutane suka bi shi suka kewaye gidan man.
Mutane suna cewa a fito fa shi a kashe shi kawai, jami'an tsaro kuwa suka ce sai dai a tafi da shi a je a bincike shi. Mutane kuma suka tirje suka ce in dai za a tafi da shi, sai dai a yi ta Kare. Bawan Allah'n da ya wallafa wannan labari a ƙafar sada zumunta na Facebook, ya ƙara da cewa, kafin ya bar gurin sai da ya shaƙi barkonon tsohuwa, har hawaye sai da ya yi kamar an kifa masa tafi.
Tuesday, May 21, 2019
Home
Unlabelled
ABIN DA NA GANI A DAI-DAI TASHAR KAWO KADUNA, YA BAN TSORO MATUƘA!
ABIN DA NA GANI A DAI-DAI TASHAR KAWO KADUNA, YA BAN TSORO MATUƘA!
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
ads1
Author Details
new platform in northern arewa
No comments:
Post a Comment