A yau Laraba ne ake sa ran shugaba Buhari zai saka
hannu a kan dokar da za ta kafa hukumar kula da sa sanƴa ido
da gudanar da makarantun sakandare a Nigeria, wato
"Secondary Education Commission", haka kuma zai sa hannu
domin rage kuɗaɗen da iyayen yara suke biya a makarantun
"Unity Collage" daga Naira dubu 83,000 zuwa Naira dubu
49,000, haka kuma zai sa hannu a kan dakatar da karɓan Naira
dubu 5,000 a matsayin kudin PTA a makarantun Unity Collage.
Karamin Ministan ilimi Mista Anthony Anwukah shi ne ya
bayyana hakan jiya a Abuja a fadar shugaban ƙasa.
Sabuwar hukumar ta "Secondary Education Commission" ita ce
mataki na farko daga cikin tsare-tsaren shugaba Buhari na
inganta ilimi daga tushe a shekaru huɗun da zai yi na ƙarshe,
Ministan ya ce, "Dokokin da muke so mu kawo a sakandaren
Nigeria mun fara su da unity college, daga nan dokokin da
sabbin tsare-tsaren ilimi zai shafi ko wacce makarantar
sakandare a ƙasar nan".
Har wa yau Ministan ya ce, "Hukumar Secondary Education
Commission za ta sake tsari wa makarantun da ake cewa FGCs
"Federal Government Collage" domin kuɗaɗen da ake cajin
iyayen dalibai ya yi tsananin da yara da dama ba su iya zuwa,
sannan hukumar za ta sa ido a kan makarantun kuɗi, wato "Private
Schools" saboda ganin irin ilimin da suke bayarwa da kuma irin
kuɗaɗen da suke karɓa a hannun iyaye".
Tuesday, May 21, 2019
Home
Unlabelled
A YAU LARABA SHUGABAN ƘASA MUHAMMADU BUHARI, ZAI SA HANNU A KAN DOKAR DA ZA TA KAFA HUKUMAR KULA DA SANƳA IDO DA GUDANAR DA MAKARANTUN SAKANDARE A NIGERIA.
A YAU LARABA SHUGABAN ƘASA MUHAMMADU BUHARI, ZAI SA HANNU A KAN DOKAR DA ZA TA KAFA HUKUMAR KULA DA SANƳA IDO DA GUDANAR DA MAKARANTUN SAKANDARE A NIGERIA.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
ads1
Author Details
new platform in northern arewa
No comments:
Post a Comment